Shugabar Sunderland ta yi murabus

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tsohon dan wasan Sunderland, Adam Johnson

Shugabar kungiyar wasa ta Sunderland, Margaret Byrne ta yi murabus daga mukaminta sakamakon kama tsohon dan wasan kulob din, Adam Johnson da laifin yin lalata da karamar yarinya.

Shi dai Adam Johnson, mai shekara 28 yana fuskantar hukuncin zaman gidan kaso tun bayan samun shi da laifin ayyuka masu alaka da lalata yarinya 'yar shekara 15.

Ana dai ta sukar kulob din na Sunderland saboda kyale dan wasan da kungiyar ta yi ya ci gaba da taka mata wasa bayan kuma an gano yana da laifi.

Byrne ta ce ta fahimci cewar kyale Johnson da ta yi ya ci gaba da taka leda "babban kuskure ne".