Arsenal: Mun yi taro a tsakaninmu - Walcott

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption 'Yan wasan Arsenal

Dan wasan Arsenal, Theo Walcott ya bayyana cewa 'yan wasan Arsenal sun yi taro ba tare da kociyansu ba, da manufar samawa kulob din makoma a gasar Premier ta wannan kakar.

Walcott ya ce " mun yi tattaunawar sirri a tsakaninmu. Taro wanda kowa ya bayyana yadda yake kallon al'amarin kungiyar kuma mun yi nasara."

Dan wasan ya kara da cewa tattaunawar za ta taimakawa kulob din wajen yin nasara duk da jan katin da aka ba wa abokin wasansu, Francis Coquelin a wasan da suka yi da Tottenham.

Arsenal din ce dai ta uku a teburin gasar Premier amma tana hankoron kofin premier karon farko a tsawon shekara 12.