Za a ƙara girman filin wasa na Nou Camp

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nou Camp shi ne mafi girma a Turai

Barcelona na shirin sake fasalin filin kwallonta mai sun Nou Camp inda zai koma cin 'yan kallo kusan dubu 105 daga nan zuwa shekara ta 2021.

Kamfanoni biyu, daya na Japan mai suna Nikken Sekkei da kuma Catalan Studio su ne suka samu kwangilar sake fasalin filin wasan na zakarun gasar La Liga.

A yanzu haka dai Nou Camp na daukar 'yan kallo fiye da dubu 99, kuma filin wasan shi ne mafi girma a Turai.

A sabon fasalin, za a lullube daukacin filin wasan da kwano ta yadda ruwa ko rana ba za su dinga bugun 'yan kwallo ba.

Za a soma aikin ne a shekarar 2017 kuma aikin ba zai hana Barcelona buga wasanninta a Nou Camp ba.