Premeir League: Za a rage kudin shiga kallo

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Magoya bayan kungiyoyi dai sun dade suna korafi kan yawan kudin shiga kwallon.

Kungiyoyin wasan kwallo na gasar Premeir ta Ingila sun amince da su rage kudin shiga kallo zuwa £30, ga magoya bayan kungiyoyin masu zuwa kallo daga nesa.

Batun tsadar kudin tikitin shiga kallon wasanni dai ya dade yana jawo kace-nace a Birtaniya.

Yanzu haka dai kungiyoyi 20 manya na gasar ta Premeir sun amince baki dayansu da a rage wa masu kallon da suke zuwa daga nesa kudin tikitin.

Magoya baya za su fara biyan £30 daga kakar wasa mai zuwa, kuma tsawon kakar wasanni uku na gaba.