Tennis: Sharapova ta fara fuskantar takunkumi

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Sharapova ta dauki kofin manyan gasar tennis ta duniya sau biyar.

Wasu kamfanoni sun sanar da yanke alaka da 'yar wasan tennis din nan, Maria Sharapova, wadda ta bayyana cewa ba ta haye gwajin da aka yi mata na shan kwayoyi masu kara kuzari ba.

A ranar Litinin ne dai Sharapova, mai shekara 28 ta fadi da bakinta cewa gwajin da aka yi mata a watan Janairu, ya nuna cewa tana shan kwayar Meldonium wadda aka haramta.

Sakamakon haka kamfanin kayayyakin wasanni na Nike da kamfanin agogo na Heuer da kuma kamfanin kera mota kirar Porsch duka sun sanar da yanke alaka da Maria.

Maria wadda 'yar kasar Rasha ce ta zamo 'yar wasan tennis din da ta fi kowacce samun kudi a duniya, a tsawon shekara 11 da suka gabata.