UEFA: PSG ta fitar da Chelsea

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Ibrahimovic ya haskaka a wasan

Paris St-Germain ta fitar da Chelsea daga gasar zakarun Turai, bayan da Zlatan Ibrahimovic ya zura kwallo a wasan da suka buga a Stamford Bridge.

Sakamakon wasanni biyu, PSG ta samu galaba a kan Chelsea da ci hudu da biyu.

Kenan PSG ta kai zagayen gabda na kusa da karshe, a yayin da Chelsea kuma sai dai ta nemi sa'a a kakar wasa mai zuwa.

Ita ma Benfica ta kai matakin zagayen gabda na kusa da karshe a gasar, bayan ta doke Zenit St Petersburg da ci uku da daya a wasanni biyu da suka fafata.

Sauran wasannin da ke tafe:15 ga watan Maris:
  • Atl Madrid V PSV Eindhoven
  • Man City V Dynamo Kiev
16 ga watan Maris:
  • Barcelona V Arsenal
  • Bayern Mun V Juventus