Kociyan Togo na kewar Adebayor

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Kociyan kungiyar wasan kwallon kafa ta Togo, Tom Saintfiet na fatan ganin Adebayor ya zo ya bugawa kasar a karawar da za su yi da Tunisia

Mai horar da 'yan wasan Togo Tom Saintfiet na fatar ganin ya shawo kan Emmanuel Adebayor ya da ya zo ya bugawa kasar a karawar da za ta yi da Tunisia domin cin kofin Africa.

Adebayor ya ce, ya na so ne ya mayar da hankalinsa a kan Crystal Palace, sabuwar kulob din da ya koma a watan Janairu, watanni goma bayan ya bar buga kwallo.

Rabon da Adebayor ya bugawa Togo kwallo tun watan Yunin shekara 2015, rahotanni na cewa dangantaka ta yi tsami tsakanninsa da Saintfiet a baya.

Saintfiet ya ce yana ganin irin nasarorin da Adebayor ke samu a Crystal Palace kuma yana fata dan wasan gaban zai canza ra'ayinsa na zuwa ya bugawa kasarsa kwallo kafin 25 ga watan Maris ranar da za su kara da Tunisia.