Benitez ya zama sabon kocin New castle

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Kocin, mai shekara 55, ya sanya hannu a kan kwantiragin shekara uku

An nada Rafael Benitez a matsayin sabon kocin Newcastle, sakamakon korar koci Steve McClaren da aka yi.

Benitez -- wanda ya taba zama kocin na Liverpool da Chelsea da Real Madrid da Inter Milan da kuma Valencia -- ya karbi ragamar kungiyar ne yayin da ake daf da fitar da ita daga rukunin gasar Firimiyar Ingila.

Kocin, mai shekara 55, ya sanya hannu a kan kwantiragin shekara uku.

A watan Janairu ne kulob din Real Madrid ya kori Benitez watanni bakwai bayan fara jan ragamarsa.

Shi kuwa Mista McClaren ya bar aikin kociyan kulob din New Castle ne bayan ya ja ragamarta na watanni tara.