Newcastle ta sallami McClaren

Hakkin mallakar hoto z
Image caption McClaren ya sha suka a Newcastle

Kungiyar Newcastle United ta Ingila ta kori kocin 'yan wasanta Steve McClaren.

Tsohon kocin na Ingila, ya samu nasara a wasanni shida cikin 28 a Newcastle, kuma kungiyar na fuskantar barazanar koma wa gasar Championship.

An yi wa McClaren ihu a lokacin da Bournemouth ta lallasa Newcastle da ci uku da daya a filin St James' Park.

Ana sa ran tsohon kocin Liverpool, Chelsea, Real Madrid da kuma Inter Milan Rafael Benitez zai maye gurbinsa.

A cikin watan Yunin bara ne McClaren ya kulla yarjejeniyar shekaru uku da Newcastle.