Lobi Stars za ta karbi bakuncin Pillars

Hakkin mallakar hoto glonpfl Twitter
Image caption Wasannin mako na shida a gasar Firimiyar Nigeria

Kungiyar Lobi Stars za ta karbi bakuncin Kano Pillars a gasar Firimiyar Nigeria wasan mako na shida a ranar Lahadi.

Lobi Stars tana da maki tara daga wasanni biyar da ta yi a gasar, yayin da Pillars ke da maki 10 a karawa biyar da ita ma ta yi a bana.

Sauran wasanni da za a fafata Sunshine Stars za ta ziyarci Giwa FC, sai MFM ta karbi bakuncin El-Kanemi Warriors da kuma karawa tsakanin IfeanyiUbah da Ikorodu United.

Kungiyar Enyimba da Nasarawa United da Warri Wolves suna buga gasar cin kofin zakarun Afirka, saboda haka ba za su fafata ba a gasar ta Firimiya a wannan makon.

Ga wasannin mako na shida da za a buga:
  • Giwa FC vs Sunshine Stars
  • FC IfeanyiUbah vs Ikorodu United FC
  • MFM FC vs El-Kanemi Warriors FC
  • Lobi Stars FC vs Kano Pillars
  • Abia Warriors vs Rangers International FC
  • Niger Tornadoes vs Rivers United FC