Norwich da Man City sun tashi 0-0

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption City za ta buga wasanta na gaba da Dynamo Kiev a gasar zakarun Turai

Norwich City da Manchester City sun tashi wasa canjaras babu ci a gasar Premier wasan mako na 30 da suka kara ranar Lahadi.

Mai tsaron ragar Norwich City, John Ruddy ya hana kwallaye biyu shiga raga wadanda Sergio Aguero ya buga masa.

Ita ma Norwich ta samu damar cin kwallo a raga inda Patrick Bamford ya buga kwallo ta bugi turke daga yadi na 25.

Da wannan sakamakon Norwich ta hada maki 25 daga wasanni 30 da ta yi, Manchester City kuwa tana da maki 51 daga karawa 29 da ta buga a gasar ta Premier.