Dan Kanawa ya buge Shagon Musan Kaduna

Image caption A turmin farko Dan Kanawa ya buge Shagon Musan Kaduna

Bahagon Dan Kanawa ya buge Shagon Musan Kaduna a turmin farko a wasan damben gargajiya da suka yi a ranar Lahadi a gidan damben Ali Zuma dake Dei-Dei a Abuja, Nigeria.

Tun da farko Dan Kanawa da Nokiyar Dogon Sani ya so su taka wasa, amma Bahagon Abban Na Bacirawa ya ce da shi za a yi, haka ma shagon Shukuran ya ce yana sha'awar ayi da shi.

Sauran wasannin da aka yi a ranar Matawallen kwarkwada da Shagon Lawwalin Gusau ta shi suka yi canjaras a turmi biyu da suka taka.

Shi kuwa Fijo bai ba ta lokaci ba wajen buge Dakakin Dakaka a turmin farko, shima Shagon Salisu a turmin farko ya doke Shagon Dandigiri.

A wasan farko da Shagon Musan Kaduna ya yi, Autan Faya ne ya kai shi kasa a turmin farko, dambe tsakanin Shagon Bata da Niga babu kisa a turmi biyu da suka yi gumurzu.

An kuma yi gumurzu tsakanin Bahagon Alin Tarara da Shagon Sarka kuma turmi biyu suka yi babu wanda ya je kasa a tsakaninsu.

Daga karshe ne aka rufe filin da wasa tsakanin Matawallen Kwarkwada da Shagon Shukurana kuma turmi biyu suka yi Shagon Amadi ya raba wasan.