United za ta sake karawa da West Ham a FA

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption United tana mataki na shida a kan teburin Premier

Manchester United ta tashi kunnen doki 1-1 da West Ham United a gasar cin kofin Kalubale wasan daf da na kusa da karshe da suka kara a Old Trafford ranar Lahadi.

West Ham United ce ta fara zura kwallo a ragar United ta hannun Dimitri Payet bayan da aka dawo daga hutun rabin lokaci.

United din ta farke kwallon da aka zura mata ne ta hannun Anthony Martial daf da za a tashi daga fafatawar.

Da wannan sakamakon Manchester United za ta ziyarci West Ham a wasa na biyu.