Lobi da Kano Pillars sun tashi wasa 2-2

Hakkin mallakar hoto HeartlandFC twitter
Image caption Sakamakon wasan mako na shida na gasar Firimiyar Nigeria

Lobi Stars ta tashi wasa da Kano Pillars 2-2 a gasar Firimiyar Nigeria wasan mako na shida da suka fafata a ranar Lahadi.

Sauran sakamakon wasannin da aka buga Giwa FC ta ci Sunshine Stars daya mai ban haushi, yayin da IfenyiUbah ta doke Ikorodu United da ci 4-1.

Abia Warriors wadda har yanzu ba a doke ta a gasar ba, ta buga 2-2 da Enugu Rangers, ita kuwa Akwa United 2-0 ta ci Plateau United.

Niger Tornadoes ta ci Rivers United 3-2, MFM kuwa ta doke El-Kanemi Warriors da ci 3-1.

Ga sakamakon wasannin mako na shida da aka buga:
  • Giwa 1-0 Sunshine
  • Ifeanyiubah 4-1 Ikorodu United
  • MFM 3-1 El-Kanemi
  • Lobi 2-2 Pillars
  • Tornadoes 3-2 Rivers United
  • Abia Warriors 2-2 Rangers
  • Akwa Utd 2-0 Plateau United