Fifa ta dakatar da jami'an Afirka ta Kudu

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Leslie Sedibe shi ne babban jami'in hukumar kwallon kafar Afirka ta Kudu a 2010 zuwa 11

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa, ta dakatar da wasu jami'an hukumar kwallon kafar Afirka ta Kudu uku kan wasan sada zumunta da ya shafi gasar cin kofin duniya ta 2010.

Fifa ta samu jami'an ne da keta dokar da'ar ma'aikata da ya shafi dukkan dokoki da dabi'a da biyayya.

An dakatar da babban jami'in hukumar kwallon kafar Afirka ta Kudu, Leslie Sedibe, daga shiga harkokin kwallon kafa zuwa shekara biyar, zai kuma biya tarar fam dubu 14 da dari daya.

Da Sedibe da Steve Goddard da kuma Adeel Carelse an dakatar da su shiga harkokin tamaula shekara biyu kowannensu.

An samu jami'an ne da laifi bayan da aka tuhumi Lindile Kika wanda a watan Oktoba aka dakatar da shi shekara shida daga shiga harkokin tamaula, ya karyata zargin da ake masa.

Hukumar kwallon kafar Afirka ta Kudu ta yi na'am da hukuncin da aka yankewa jami'an.