Leicester ta ci gaba da zama kan teburin Premier

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Leicester City ta ci gaba da zama a mataki na daya a kan teburin Premier

Leicester City ta doke Newcastle United da ci 1-0 a gasar Premier wasan mako na 30 da suka buga a ranar Litinin.

Leicester ta ci kwallon ne ta hannun Okazaki a minti na 25 da fara tamaula.

Doke Newcastle da Leicester ta yi shi ne karon farko da aka doke Rafael Benitez a wasan farko da ya jaroranci kungiya.

Da wannan sakamakon Leicester City ta ci gaba da zama a mataki na daya a kan teburin Premier da maki 63, ita kuwa Newcastle tana da maki 24 a matsayi na 19.