Southampton ta daukaka kara kan jan kati

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Southampton ta ce bai kamata a bai wa Sadio Mane jan kati ba

Southampton ta shigar da kara kan a soke jan katin da aka bai wa Sadio Mane a wasan gasar Firimiya da suka doke Stoke City 2-1 a ranar Asabar.

Alkalin wasa Lee Mason ne ya sallami Mane bisa cin kasuwar sama da ya yi da dan kwallon Stoke Erik Pieters a cikin karin lokacin da za a tashi wasan.

Kociyan Southampton, Ronald Koeman, ya ce an samu kuskuren korar dan wasansa ne daga alkalin wasa ko kuma daga mataimakansa.

Ya kara da cewar Mane ya yi kokari ya saka kansa ne, kuma shi da kansa Pieters ya ce babu wani laifin da aka yi masa.

Shi kuwa kociyan Stoke City, Mark Hughes, ya ce shi ma ya yi mamaki da aka korin Mane kamar yadda kowa ya yi.