Toure zai buga karawa da Dynamo Kiev

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Man City na fatan kai wa wasan daf da na kusa da karshe a karon farko

Dan kwallon Manchester City, Yaya Toure, ya murmure daga jinyar da ya yi, zai kuma buga karawar da za su yi da Dynamo Kiev a gasar cin kofin zakarun Turai.

Toure mai shekara 32, dan wasan tawagar Ivory Coast bai buga karawar da City ta tashi wasa babu ci da Norwich a gasar Premier ranar Asabar ba, sakamakon raunin da ya ji.

Kociyan City, Manuell Pellegrini, wanda ke fatan jagorantar kungiyar kai wa wasan daf da na kusa da karshe a gasar ya ce Toure zai iya wasa domin ya murmure.

City ce ta doke Dynamo Kiev da ci 3-1 a Ukraine, za kuma ta karbi bakuncin wasa na biyu a Ettihad a ranar Talata.

Sai dai kuma Pellegrini ya ce ya kamata 'yan wasansa sukara kaimi fiye da wanda suka yi a karawar farko a Ukraine.