Barcelona za ta karbi bakuncin Arsenal

Image caption Barcelona ce ta daya a kan teburin La Liga da maki 75

Arsenal za ta ziyarci Nou Camp domin karawa da Barcelona a wasan gasar cin kofin zakarun Turai wasa na biyu a ranar Laraba.

A wasan farko da suka buga a Emirates, Barcelona ce ta samu nasara da ci 2-0, kuma Lionel Messi ne ya ci kwallayen.

A karshen mako ne Watford ta fitar da Arsenal daga kofin FA, kuma Gunners din ta koma mataki na uku a kan teburin Premier.

Ita kuwa Barcelona kwallaye shida da babu ta ci Getafe a wasan gasar La Liga mako na 29 da suka buga a ranar Asabar, kuma Barca ce a kan teburin na Spaniya da maki 75.

Ba a doke Barcelona a wasanni 37 a jere ba a dukkan karawar da ta yi, rabon da ta yi rashin nasar tun lokacin da Seville ta ci ta 2-1 a ranar 3 ga watan Oktoban 2015 a gasar La Liga.