Wa zai lashe kyautar zura kwallaye a Premier

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Vard da Kane sun ci kwallye 19 a gasar ta Premier bana

Leicester City ta ci gaba da zama a mataki na daya a kan teburin Premier ta kuma bai wa Tottenham wadda ke matsayi na biyu tazarar maki biyar.

Sai dai kuma dan wasan Leicester City, Jamie Vardy bai ci kwallo ba a wasan da suka doke Newcastle United 1-0, har yanzu yana da kwallaye 19 da ya zura a raga a gasar.

Shi ma dan kwallon Tottenham Harry Kane ya ci kwallaye 19, yayin da Romelu Lukaku dan wasan Everton keda kwallaye 18 da ya ci a gasar ta Premier.

Dan wasan Manchester City, Sergio Aguero wanda ya lashe kyutar bara da yawan kwallaye 26 ya ci 16 a bana.

Jumulla dai kwallaye 768 aka ci a gasar ta Premier bana, bayan da aka buga wasannin mako na 30.