Premier: 'Akwai sauran rina a kaba'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Vardy na daga cikin manyan 'yan wasan Leicester

Kocin Leicester Claudio Ranieri ya hakikance cewa har yanzu akwai sauran rina a kaba, a yayin da ake ci gaba da fafutuka a kokarin lashe gasar Premier.

Leicester ta bai wa Tottenham tazarar maki biyar a saman tebur gasar, bayan da ta samu galaba a kan Newcastle da ci daya da nema

Ranieri ya ce "Har yanzu babu tabbas a kan kungiyar da za ta lashe gasar."

"A yanzu za mu mayar da hankali a kan wasanmu da Crystal Palace," in ji Ranieri.

Masu sharhi da dama na ganin cewa Leicester City za ta iya lashe gasar ta bana.