An kori 'yan wasa 9 a gasar Firimiyar Nigeria

Hakkin mallakar hoto thenff
Image caption A ranar Asabar ne za a ci gaba da buga wasannin mako na bakwai na gasar

Kimanin 'yan wasa tara aka kora aka kuma bai wa 189 katin gargadi a lokacin da ake wasannin gasar Firimiyar Nigeria, bayan da aka buga wasan mako na shida.

Tony Okpotus ne ke kan gaba a yawan cin kwallaye a gasar inda ya ci biyar, Sai Wasiu Jimoh na shooting Stars wanda ya ci hudu a matsayi na biyu.

Kungiyar MFM ce ke mataki na daya a kan teburi da maki 13, sai Enugu Rangers da maki 11, Kano Pillars ma maki 11 ta samu.

IfeanyiUbah da Lobi Stars da Abia Warriors kowannensu yana da maki 10.

A ranar Laraba ne Akwa Utd za ta karbi bakuncin Ikorodu Utd a kwantan wasan mako na biyu da ba su buga ba a baya.