'Newcastle za ta ci gaba da zama a Premier'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Wannan ne karon farko da Benitez ya yi rashin nasara a wasan farko da ya jagoranci sabuwar kungiya

Sabon kociyan Newcastle United, Rafael Benitez, ya ce kulob din zai ci gaba da zama a gasar Premier, duk da doke su 1-0 da Leicester ta yi ranar Litinin.

Leicester City ce ta samu nasara a kan Newcastle da ci daya mai ban haushi a wasan Premier gasar mako na 30 kuma Osazaki ne ya ci kwallon.

Benitez ya ce idan 'yan wasansa suka ci gaba da taka rawa kamar wadda suka yi da Leicester, lallai za su ci gaba da buga Premier ta badi.

United tana mataki na 19 a kan teburi da maki 24, kuma saura wasanni tara suka rage a kammala gasar Premier bana.

A ranar Lahadi ne Newcastle za ta karbi bakuncin Sunderland wadda ke mataki na 17 kan teburi da maki 25.