Barca ta fitar da Arsenal daga kofin UEFA

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Karo na tara Barcelona tana kaiwa wasan daf da na kusa da karshe kenan

Barcelona ta doke Arsenal da ci 3-1 a gasar cin kofin zakarun Turai, ta kuma kai wasan daf da na kusa da karshe a gasar.

Neymar ne ya fara ci wa Barcelona kwallon farko a minti na 18 da fara tamaula, Arsenal ta farke kwallon ta hannun Elneny bayan da aka dawo daga hutu.

Barcelona wadda ta lashe kofin zakarun Turai karo biyar ta ci kwallo ta biyu ne ta hannun Suarez da kuma ta uku ta hannun Lionel Messi.

Da wannan nasarar da ta samu, yanzu Barca ta yi wasanni 38 a jere ba tare da an doke ta ba a dukkan wasannin da ta yi a gasar bana.