FA ba za ta hukunta Costa kan harara ba

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Everton ce ta fitar da Chelsea daga gasar cin kofin kalubale

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ba za ta hukunta dan wasan Chelsea Diego Costa, bisa harara da ya yi wa magoya bayan Everton a wasan cin kofin FA.

Sai dai kuma hukumar ta tambayi Costa dalilin da ya sa ya yi hararar a lokacin da zai fita daga filin, bayan da aka tafi hutun rabin lokaci.

Bayan da hukumar ta ji bahasin dan kwallon ne ta yanke cewar bai yi wani laifin da za ta hukunta shi ba.

Sai dai kuma hukumar ta tuhumi dan wasan kan halin rashin da'a a lokacin da ya ki fita daga filin wasa bayan da aka bashi jan kati.

An bai wa Costa damar kare kansa daga tuhumar da FA ke yi masa a karawar da Everton ta ci Chelsea 2-0 a gasar wasan cin kofin kalubale.