Fifa za ta kwato 'miliyoyin daloli'

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Akwai kalubale a gaban sabon shugaban Fifa, Infantino

Hukumar kwallon kafa ta duniya, Fifa na kokarin kwato 'miliyoyin daloli' da ake zargin tsaffin jami'anta sun yi awon gaba da su.

Tsaffin jami'an Fifa Chuck Blazer, Jack Warner da kuma Jeffrey Webb na daga cikin mutanen da ake tuhumar bisa zargin almundahana.

Tun a cikin watan Mayun 2015, Fifa ta shiga rudu saboda zarge-zargen cin hanci da rashawa.

A halin yanzu dai jami'ai 41 ke fuskantar tuhuma daga hukumomin Amurka kan batutuwan da suka jibanci rashawa a Fifa.

A watan Fabarairu ne, Gianni Infantino ya dare kujerar shugabancin Fifa bayan da aka dakatar da Sepp Blatter kan zarge-zargen rashawa.