An soke jan karin da aka bai wa Mane

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Mane zai buga wa Southampton wasan Premier da za ta yi da Liverpool ranar Lahadi

Hukumar kwallon kafa ta Ingila ta soke jan katin da aka bai wa Sadio Mane dan kwallon Southampton, sakamakon shigar da kara da ta yi.

Hukumar ta ce bai kamata a kori dan wasan ba a karawar da Southampton ta doke Stoke City 2-1 a gasar Premier a karshen mako.

Alkalin wasa Lee Mason ne ya sallami Mane bisa cin kasuwar sama da ya yi da dan kwallon Stoke Erik Pieters a cikin karin lokacin da za a tashi wasan.

Kociyan Southampton, Ronald Koeman, ya ce an samu kuskuren korar dan wasansa ne daga alkalin wasa ko kuma daga mataimakansa.

Ya kara da cewar Mane ya yi kokari ya saka kansa ne, kuma shi ma dan wasa Pieters ya ce babu wani laifin da aka yi masa.