FIFA: Blatter ya kai kara kotu

Hakkin mallakar hoto AFP
Image caption Blatter da Platini

Tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya, FIFA, Sepp Blatter ya kai kara kotun kwallon kafa ta duniya kan dakatar da shi da aka yi daga buga wasanni bisa tuhumar cin hanci.

An dai dakatar da Blatter ne tare da tsohon shugaban hukumar kwallon kafa ta turai, Michel Platini bisa bayarwa da karbar cin hanci na $2m.

Kotun ta tabbatar da karar da Blatter ya shigar a gabanta.

Blatter da Platini dai sun sanar cewa za su daukaka kara zuwa kotun bayan da kwamitin da'a na fifa ya ki janye dakatarwar da aka yi musu na shekara 8, duk da cewa an rage wa'adin zuwa shekara shida ga kowannen su.