"A shirye nake na kara da kowacce kungiya"

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Bayern Munich ta samu kai wa wasan daf da na karshe

Kociyan Bayern Munich Pep Guardiola ya ce bai sa damuwa a ransa ba ko da wacce kungiya za su kara a wasan daf da da na kusa da na karshe na gasar Zakarun Turai, bayan da suka doke Juventus.

Guardiola ya ce, "In har kana son ka samu kai wa wasan daf da na karshe to dole ne ka shirya samun nasara kan abokan karawarka."

Ya kara da cewa, "Amma sai gashi mun kai ga ci, mun yi nasara cikin minti daya kafin wasa ya tashi amma da an cire mu."

Sauran kungiyoyi bakwai din da suka buga wasanni a wasan daf da na kusa dana karshe sun hada da Manchester City da Paris St-Germain da Wolfsburg da Benfica da Atletico Madrid da Real Madrid da da kuma Barcelona.