Uefa na tuhumar United da Liverpool

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Liverpool ta fitar da United a gasar

Hukumar kwallon kafa ta Turai, Uefa na tuhumar kungiyoyin Manchester United da Liverpool sakamakon rikicin da ya balle lokacin wasan gasar Europa.

An ga magoya bayan kungiyoyin suna fada a wajen da aka kebe don zamansu, inda suka yi kaca-kaca da filin wasan, al'amarin da ya sa aka kama mutane biyar.

Ana dai tuhumar dukkannin kungiyoyin da jawo husuma da jefe-jefe a filin wasan.

Ana tuhumar Liverpool wadda ta ci Manchester United 3-1, da yin iface-iface da kuma yin wasa da wuta.

Kwamitin da'a na Uefa ne zai saurari karar a ranar 19 ga watan Maris.