Uefa: City za ta hadu da PSG

Hakkin mallakar hoto AP
Image caption City ce ta lashe gasar Capital One a 2016

Manchester City za ta hadu da zakarun kwallon Faransa, Paris St-Germain a zagayen gabda na kusa da karshe a gasar Zakarun Turai.

City ce kungiyar Ingila da ta rage a gasar, bayan da aka fitar da Arsenal, Chelsea da kuma Manchester United.

Ita kuma Barcelona za ta fafata ne da Atletico Madrid a yayin da Bayern Munich za ta kara da Benfica sai kuma Real Madrid ta fafata da Wolfsburg.

Za a buga wasannin gabda na kusa da karshen ne a ranakun 5-6 ga watan Afrilu da kuma 12-13 ga watan Afrilu.

Jadawalin:
  • Wolfsburg v Real Madrid
  • Bayern Munich v Benfica
  • Barcelona v Atletico Madrid
  • Paris St-Germain v Manchester City