Arsenal ta doke Everton 2-0 a Premier

Hakkin mallakar hoto Rex Features
Image caption Arsenal ta hada maki 58 daga wasanni 31 da ta buga a Premier

Everton ta yi rashin nasara a hannun Arsenal da ci 2-0 a gasar cin kofin Premier wasan mako na 31 da suka kara a Goodison Park.

Danny Welbeck ne ya fara ci wa Arsenal kwallo a minti na bakwai da fara tamaula, sannan matashin dan wasa Alex Iwobi ya ci ta biyu a wasan farko da ya fara yi wa Gunners.

Da wannan sakamakon da Arsenal ta samu ya sa ta hada maki 53, yayin da Everton na nan da makinta 38 a gasar ta Premier.

Arsenal za ta buga wasan mako na 32 ne da Watford wadda ta fitar da ita daga gasar cin kofin FA.