Enyimba ta kai zagayen gaba a kofin zakaru

Hakkin mallakar hoto Enyimba FC Twitter
Image caption Enyimba ta kai wasan zagayen gaba a gasar cin kofin zakarun Afirka

Kungiyar Enyimba ta Nigeria ta kai wasan zagayen gaba a gasar cin kofin zakarun Afirka wato CAF Champions League.

Enyimba ta yi rashin nasara ne a hannun Vitalo ta Burundi da ci 2-1 a karawa ta biyu da suka yi a Burundi a ranar Asabar.

A wasan farko da suka buga a Nigeria Enyimba ce ta doke Vitalo da ci 5-1.

Da wannan sakamakon da Enyimbar ta samu ya sa ta kai wasan zagayen gaba da zai kunshi kungiyoyi 16 da za su rage a gasar.