Tennis: Nadal ya kai wasan daf da karshe

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Nadal ya lashe kofin a 2007 da 2009 da kuma 2013

Rafael Nadal a karon farko ya doke Kei Nishikori wanda ke mataki na 10 a jerin wadanda suka fi iya wasan kwallon tennis a duniya.

Nadal din ya samu nasara ne a kan Nishikori na Japan da ci 6-4 da kuma 6-3 wanda hakn ya sa ya kai wasan daf da karshe a gasar tenis da ake yi a Indiana Wells.

Nadal dan kasar Spaniya zai fafata ne da Novak Djokovic wanda ya ci Jo-Wilfried Tsonga na Faransa 7-6 (7-2) 7-6 (7-2)

Rafael Nadal shi ne ya lashe gasar a 2007 da 2009 da kuma 2013