Bayern Munich na daf da lashe Bundesliga

Image caption Bayern Munich tana da maki 69 a gasar Bundeslia a mataki ta daya

Bayan Munich na daf da daukar kofin Bundesliga na hudu a jere, bayan da ta ci FC Cologne 1-0 a wasan mako na 27 da suka kara a ranar Asabar.

Munich din ta ci kwallonta ne ta hannun Robert Lewandowski, kuma ta 25 jumulla da ya zura a gasar Bundeslida ta bana.

Cologne ta kusa farke kwallon da aka zura mata ta hannun Anthony Modeste da kuma damar da Leonardo Bittencourt ya samu bayan da aka dawo daga Hutu.

Munich ta bai wa Borussia Dortmund wadda za ta ziyarci Augsburg ranar Lahadi tazarar maki takwas.