Man United ta doke Man City da ci 1-0

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Rashford yana da shekara 18 da kwanaki 141 ya ci City kwallo

Manchester City ta yi rashin nasara a hannun makwabciyarta Manchester United da ci daya mai ban haushi a gasar Premier wasan mako na 31 da suka yi ranar Lahadi.

United din ta ci kwallonta ne ta hannun Marcus Rashford a minti na 14 da fara tamaula a filin wasa na Ettihad.

Kwallon Rashford ya ci ya zama matashin dan wasa da ya ci kwallo a wasan hamayya tsakanin kungiyoyin biyu, yana da shekara 18 da kwanaki 141.

Nasarar da United ta samu ya sa ta samu maki 50 tana mataki na shida a kan teburin Premier, City kuwa tana da makinta 51 a matsayi na hudu a kan teburin.

Manchester City za ta ziyarci Bournemouth a wasan Premier na gaba, inda Manchester United za ta karbi bakuncin Everton a Old Trafford.