Southampton ta doke Liverpool da ci 3-2

Image caption Southampton tana mataki na bakwai a kan teburin Premier

Southampton ta samu nasara a kan Liverpool da ci 3-2 a gasar Premier wasan mako na 31 da suka fafata a ranar Lahadi.

Liverpool ce ta fara cin kwallo ta hannun Coutinho a minti na 17 da fara wasa sai Sturridge ya kara ta biyu a minti na 22.

Southampton ta farke kwallayen da aka zura mata ne ta hannun Sadio Mane a minti na 64, sannan Pelle ya ci ta biyu, kuma Mane ya kara ta uku saura minti hudu a tashi daga wasan.

Southampton wadda ta samu nasara a karawar tana mataki na bakwai a kan teburin Premier da maki 47.

Ita kuwa Liverpool da ta yi rashin nasara wadda ta yi wasanni 29 a gasar tana matsayi na tara da maki 42.