Tottenham ta samu nasara a kan Bournemouth

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Tottenham tana mataki na biyu a kan teburin Premier

Bournemouth ta yi rashin nasara a hannun Tottenham da ci 3-0 a gasar Premier wasan mako na 31 da suka kara a ranar Lahadi.

Kane ne ya fara cin kwallo a minti guda da fara tamaula, shi ne ya kuma kara ta biyu a minti na 16, daga baya Eriksen ya ci ta uku.

Kwallayen da Kane ya ci ya sa ya zama dan wasan da ya fi cin kwallaye a gasar ta Premier bayan da aka yi wasanni 31, inda ya ci 21.

Tottenham tana mataki na biyu a kan teburin Premier, kuma Leicester wadda ke mataki na daya tana da tazarar maki biyar.

A wasan farko a gasar Premier da suka yi a bara a Tottenham ce ta samu nasara da ci 5-1.