An ci kwallaye 135 a gasar Firimiyar Nigeria

Hakkin mallakar hoto NPFL Twitter
Image caption Kwallaye 17 aka ci a mako na bakwai a gasar Firimiyar Nigeria

An zura kwallaye 135 a gasar Firimiyar Nigeria, bayan da aka kammala wasannin mako na bakwai a gasar.

A wasannin mako na bakwai da aka yi a ranar Asabar da Lahadi, an ci kwallaye 17 daga cikin wasanni bakwai da aka yi.

A dai makon ne kungiyoyi shida da suka yi wasanninsu a gida suka samu nasara, sai kulob daya da ya lashe wasa a waje, ba a buga canjaras ba.

Kungiyar Enugu Rangers ce ke mataki na daya a kan teburi da maki 14, Sai MFM a matsayi na biyu da maki 13, inda Kano Pillars wadda ta yi wasanni shida tana matsayi na uku da maki11.