Wasu 'yan kallo sun mutu a gasar Morocco

Image caption Mutane biyu ne suka mutu sakamakon fadan da ya barke a gasar cin kofin Morocco

'Yan kallon kwallon kafa biyu ne suka mutu a lokacin da yamutsi ya barke a wasan da aka buga a gasar cin kofin kasar Morocco.

Fada ya barke ne tsakanin magoya bayan Raja de Casablanca a wasan da ta doke Chabab Rif Al Hoceima da ci 2-1.

Magoya bayan sun yi ta jifa da wasu abubuwa masu tartsatsin wuta da karya kujerun zama na filin wasan Mohammed na hudu.

Wani jami'in tsaro ya ce an kama kimanin mutanen 31 da suke da hannu wajen tada yamutsi da bannata kayayyakin filin wasa.

Hukumar kwallon kafa ta Morocco ta dakatar da magoya bayan Raja daga shiga kallon wasannin kungiyar biyar da za ta yi a gida, kuma za ta biya tarar sama da fam 7,000.