U-23: Nigeria za ta kara da Brazil

Hakkin mallakar hoto TheNFF twitter
Image caption Brazil za ta karbi bakuncin Nigeria a wasan sada zumunta ranar Alhamis

Kociyan tawagar matasa 'yan kasa da shekara 23 ta Nigeria, Samson Siasia ya gayyaci 'yan wasa 20, domin karawa da Brazil a wasan sada zumunta.

Brazil ce za ta karbi bakuncin Nigeria a wasan sada zumunta a ranar Alhamis, domin shirin tunkarar wasan kwallon kafa a gasar Olympic.

Cikin tawagar da aka gayyata sun hada da matasan 'yan wasa da suke taka leda a Nigeria guda tara da kuma masu murza leda a wajen kasar su 11.

Kociya Siasia, shi ne yake rike da tawagar Super Eagles a matsayin rikon kwarya, zai kuma jagoranci tawagar a karawa da Masar a ranar Juma'a.

Nigeria za ta karbi bakuncin Masar a wasan farko a neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da za suyi a Kaduna, Nigeria.

Ga jerin 'yan wasan da aka gayyata domin karawa da Brazil:

1. Emmanuel Daniel

2. Yusuf Mohammed

3. Sincere Seth

4. Segun Oduduwa

5. Chizoba Amaefule

6. Ndifreke Effiong

7. Stanley Dimgba

8. Ubong Ekpai

9. Victor Osimhen

10. Sodiq Popoola

11. Godswill Ekpolo

12. Nathan Oduwa

13. Junior Ajayi

14. Taiwo Awoniyi

15. Imoh Ezekiel

16. Agboyi Ovbokha

17. Musa Mohammed

18. Theophilous Solomon

19. Saturday Kaego

20. Iyayi Believe