Mbokani bai ji rauni ba a harin Brussels

Hakkin mallakar hoto epa
Image caption Mbokani bai ji rauni ba ya kuma isa gida lafiya in ji Norwich City

Dan wasan Norwich, Dieumerci Mbokani, bai ji rauni ba a harin bam din da aka kai a filin jirgin sama da ke Brussels.

Mbokani, yana filin jirgin saman a lokacin da bama-bamai biyu suka tashi, kuma Norwich ta ce dan wasan ya isa gida lafiya.

Firai ministan Belgium, ya ce mutane da dama ne suka mutu wasu da yawa kuma sun sami munanan raunuka a lokacin da aka kai harin ta'addanci.

Kungiyoyin kwallon kafa na Belgium sun soke wasannin atisaye da suka shirya buga a ranar Talata, domin girmama wadanda harin ya rutsa da su.

Watakila a soke wasan sada zumunta da kasar za ta yi da Portugal a filin wasa na King Baudouin a ranar 29 ga watan Maris.