West Ham za ta kara da United ranar Laraba

Image caption West Ham tana mataki na biyar a kan teburin Premier, United tana mataki na shida

West Ham United za ta karbi bakuncin Manchester United a wasa na biyu na gasar cin kofin Kalubale a ranar Laraba 13 ga watan Afirilu.

A karawar farko a wasan daf da na kusa da karshe da suka fafata a Old Trafford tashi suka yi kunnen doki 1-1.

Duk wanda ya yi nasara a fafatawar zai fuskanci Everton a wasan daf da na karshe a ranar Asabar 23 ga watan Afirilu a Wembley.

A wasa na biyu na daf da karshe a gasar FA din Crystal Palace ce za ta yi gumurzu da Watford a ranar 24 ga watan Afirilu a Wembley.