Ja gaba a cin kwallaye a Firimiyar Nigeria

Hakkin mallakar hoto NPFL Twitter
Image caption Za a ci gaba da wasannin mako na takwas a gasar Firimiyar Nigeria

Dan wasan Lobi Stars Anthony Okpotu ne ke kan gaba a matsayin wanda yafi cin kwallaye a gasar Firimiyar Nigeria.

Bayan da aka buga wasannin sati na bakwai a karshen mako da ya wuce, Okpotu, ya ci kwallaye shida a gasar.

Wasiu Jimoh na kungiyar 3SC shi ne na biyu a yawan cin kwallaye a gasar, wanda ya ci biyar a raga.

Dan wasan Niger Tornadoes, Isma'ila Gata ya ci kwallaye hudu kuma yana mataki na uku a jeren 'yan wasan da suke kan gaba a zura kwallaye a gasar.

An zura kwallaye 135 jumulla a gasar ta Firimiyar Nigeria, kuma a wasannin mako na bakwai da aka yi a ranar Asabar da Lahadi, an ci kwallaye 17 daga cikin wasanni bakwai da aka yi.