Leicester za ta fafata da Barca da PSG

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Leicester ce ke mataki na daya a kan teburin Premier da maki 66

Leicester City za ta kara da Barcelona da Paris St-Germain a gasar cin kofin Champions, domin shirin tunkarar wasannin badi.

Leicester za ta fafata da Celtic a Glasgow ranar 23 ga watan Yuli, sai kuma ta kara da PSG a Los Angeles ranar 30 ga watan Yulin, ta kuma yi gumurzu da Barcelona a Stockholm ranar 3 ga watan Agusta.

Leicester wadda ke kan teburin Premier tana daga cikin kungiyoyin Premier biyar da za su fafata a wasannin atisayen tunkarar gasar badi da za a yi yawancin karawar a Amurka.

Liverpool za ta kara da Chelsea a filin wasa na Rose Bowl da ke Pasadena ranar 27 ga watan Yuli, Liverpool din dai za ta fafata da AC Milan a Santa Clara a California ranar 30 ga watan Yuli, sannan ta fuskanci Barcelona ranar 6 ga watan Agusta.

Chelsea kuwa za ta kara ne da Real Madrid ranar 30 ga watan Yuli, sannan ta kuma fafata da AC Milan a Minneapolis ranar 3 ga watan Agusta.

Kungiyoyi 10 da za su yi gumurzu a wasannin, sun hada da Bayern Munich, yayin da Manchester United za ta yi atisaye ne a China, ita kuwa Tottenham Australia za ta ziyarta.

Ga jadawalin wasannin da za a yi:

23 Juli - Celtic v Leicester, Glasgow

24 Juli - Inter v PSG, Eugene

27 Juli - Real Madrid v PSG, Columbus

27 Juli - Bayern Munich v AC Milan, Chicago

27 Juli - Chelsea v Liverpool, Pasadena

30 Juli - Celtic v Barcelona, Dublin

30 Juli - Inter v Bayern Munich, Charlotte

30 July - AC Milan v Liverpool, Santa Clara

30 July - PSG v Leicester, LA

3 Agusta - Barcelona v Leicester, Stockholm

3 Agusta - Bayern Munich v Real Madrid, East Rutherford

3 Agusta - AC Milan v Chelsea, Minnapolis