Schweinsteiger ya ji rauni a gwiwarsa

Hakkin mallakar hoto Getty
Image caption Jamus za ta kara da Ingila da kuma Italiya a wasannin sada zumunta

Dan wasan Manchester United, Bastian Schweinsteiger, ba zai buga wa Jamus wasan sada zumunta da Ingila ba, sakamakon raunin da ya ji.

Jamus za ta karbi bakuncin Ingila a wasan sada zumunta da za su kara a ranar Asabar da yammaci.

Haka kuma Schweinsteiger, ba zai buga wa tawagar Jamus wasan sada zumunta da za ta fafata da Italiya ba.

Kociyan Jamus, Joachim Loew, ya ce raunin Schweinsteiger ya munana, ba zai iya buga tamaula ba.

Kociyan ya kuma ce ba zai iya cewa ga ranar da dan kwallon mai shekara 31 zai murmure ba.