Ban san me na yi wa Klopp ba — Benteke

Hakkin mallakar hoto PA
Image caption Liverpool tana mataki na tara a kan teburin Premier da maki 44

Dan wasan Liverpool, Christian Benteke, ya ce ya rasa dalilan da ya sa kociya Jurgen Kloop ya ke watsi da shi ba.

Benteke mai shekara 25, ya buga wa Liverpool wasanni biyar ne daga cikin 16 da Klopp ya jagoranci kungiyar tun komawarsa Anfield da horar da tamaula.

Klopp ya ce ya yi wa dan wasan maganganu, ba wani abu. An nuna kociyan ya ji haushin kasa cin kwallo da Benteke ya yi a karawar da Southampton ta ci Liverpool 3-2 a gasar Premier ranar Lahadi.

Benteke ya ce tun a watan Janairu baya son barin Anfield, kuma har yanzu yana son ya taka rawar gani a kulob din.

Benteke, tsohon dan wasan Aston Villa ya ci wa Liverpool kwallaye takwas daga wasanni 35 da ya yi tun sanda ya koma Anfield da murza leda a Yulin 2015.