Sudan ta Kudu ta bude ofishin kwallon kafa

Image caption A shekarar 2011 ne Sudan ta Kudu ta fara buga tamaula a hukumance

Shugaban hukumar kwallon kafa ta duniya Fifa, Gianni Infantino, ya bude sabon ofishin hukumar kwallon kafa ta Sudan ta Kudu a ranar Laraba.

Infantino, wanda ya maye gurbin Sepp Blatter, ya bude ofishin ne a babban birnin kasar da ke Juba.

Zai kuma halarci wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin nahiyar Afirka da Sudan ta Kudu za ta karbi bakuncin Benin ranar Laraba.

Sudan ta Kudu ta fara buga wasanta na farko a hukumance a karawar da ta yi da Uganda a wasan sada zumunta a cikin watan Yulin 2012.

Shi ne kuma babban wasan da kasar ta buga tun samun yancin kai da ta yi daga wajen Sudan.