Suarez zai yi wa Uruguay wasa bayan cizo

Hakkin mallakar hoto Reuters
Image caption Suarez ya yi cizon ne a lokacin da Uruguay ke wasa da Italy a Brazil

Luis Suarez ya kammala hukuncin dakatar da shi daga buga tamaula da aka yi , saboda cijon da ya yi wa Giorgio Chiellini a gasar cin kofin duniya.

Dan wasan ya ce yana ta kokarin koyar yadda zai dunga kwantar da hankalinsa idan yana murza leda a fili.

Uruguay tana mataki na biyu a kan teburi biye da Ecuador a wasannin neman burbin shiga gasar cin kofin duniya, za kuma ta kara da Brazil ranar Juma'a.

An dakatar da Suarez daga buga wa Urugauy manyan wasanni tare da kuma hana shi shiga sabgogin tamaula tsawon watanni hudu.

Suarez bai buga wa kasarsa wasanni ba tsawon kwanaki 640 da karawar da Colombia ta doke Urugauy a gasar kofin duniya da wasannin gasar Copa America da karawa hudu da kasar ta yi a fafatawar neman tikitin shiga gasar cin kofin duniya ta 2018.

Suarez wanda ke taka leda a Barcelona an amince ya buga wa Urugauy wasannin sada zumunta a lokacin.