Nigeria za ta kara da Egypt a Kaduna

Hakkin mallakar hoto the nff twitter
Image caption Super Eagles za ta kara da Masar a Kaduna a ranar Juma'a

Tawagar kwallon kafa ta Nigeria za ta kara da ta Masar a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Afirka a jihar Kaduna, ranar Juma'a.

Super Eagles ta kara da The Pharaohs a manyan wasanni guda 15, inda Nigeria ta ci karawa biyar, Masar ta lashe hudu suka yi canjaras sau shida.

Nigeria da Masar ba su sami gurbin buga gasar cin kofin nahiyar Afirka da aka yi a Equotorial Guinea ba a 2015, wanda Ivory Coast ta dauki kofin.

Nigeria ta lashe kofin nahiyar Afirka sau uku, yayin da Masar ta dauka sau bakwai

Masar za ta karbi bakuncin Nigeria a wasa na biyu a ranar Talata 29 ga watan Maris.

Gabon ce za ta karbi bakuncin wasannin cin kofin nahiyar Afirka da za a fara a cikin watan Janairu zuwa Fabrairun 2017.